Monday, April 6, 2020

Tarbiyyar Yara A musulinci Malama Na 1

Tarbiyyar Yara A musulinci Tare Da Malama Shugaban Nisa'us-sunnah Ta Kasa Baki Daya


 

Karkashin Jagorancin Shugaban Izala Na Africa Baki Daya Sheikh Abdullahi Bala Lau Nigeria Wa'azin Yagata Ne Agarin Kaduna Nigeria zamu chigaba da kawo muku Tarbiyyar Yara na sauran malamai kamar malam kabiru gombe shima yayi karatun Tarbiyyar Yara malam aminu ibrahim daurwa shima yayi karatun Tarbiyyar Yara Malam umar shehu zaria shima yayi karatun Tarbiyyar Yara malam  malam musa yusuf asadus-sunnah shima yayi karatun Tarbiyyar Yara  malam

 

 

Takaitaccen tarihin kungiyar IZALA


KADAURE KA KARANTA


DON KU
AMFANA


Jama’atu Izatil Bid’ah Wa Iqamatus Sunnah (Jibwis)
Kungiyar kawar da Bidi’ah da tsayar da sunna
Wannan qungiya ta al’ummar musulmi an kafa ta ne tun a shekarar 1978 a
Najeriya, kuma shugabanta na farko shi ne Alhai Musa Gandu Muhammad, a
qarqashin kulawar Malam Abubakar Mahmud Gumi, tare da Sheikh Isma’il Idris bn
Zakariyya, a matsayin shugaban majalisar malamai na farko na kungiyar.
Qungiyar ita ce irinta ta farko a tarihin yada addinin musulunci a Najeriya, hadi da
harkar ilmantarwa, tare da daukaka darajar harkokin addinin Musulunci ba tare da
wani tsoro ba. Don haka ne sai kungiyar ta sanya wasu ginshiqan manufofi da take
so ta cimma domin kai wa ga gaci.


Daga cikin muhimman manufofin wannan kungiya sun hada da
Kawar da duhun jahilci daga cikin al’umma, wanda ya yi wa al’umma katutu.


Hada kan al’ummar musulmi a bisa koyarwar Alqur’ani da Sunnar Manzon Allah
(SAW),
Wayar da kan al’ummar musulmi game da al’amuran addini, domin a gudu tare a
tsira tare.


Fadakar da al’ummar musulmi domin a yi watsi da wasu miyagun littattafai da
suke tura mutane cikin halaka.


Tabbatarwa da cewa Annabi (SAW) ya kammala isar da sakon Allah (SWT).


Duk wanda ya yi da’awar annabta, ko kuma yake riya cewa Annabi (SAW) yana
ziyartarsa da wani sako, to wannan zunzurutun makaryaci ne.


Yada Musulunci a Najeriya da wajen Najeriya.


Yin da’awa a kan fadin Manzon Allah (SAW) cewa: “duk wanda ya ga abin qi, to
ya sauya shi da hannunsa, idan ba zai iya ba, to da harshensa, in ba zai iya ba, to
da zuciyarsa, amma wannan shi ne mafi raunin imani.


Kar a boye hujja in dai har ta tabbata daga littafin Allah Madaukakin Sarki, ko
sunnar Manzon Allah (SAW).


Wasu daga cikin ayyukan kungiyar sun hada da:
Kasancewar wannan kungiya ta shahara sosai a kasashe daban-daban na duniya,
wannan ya sa aka samar da kwamitoci daban-daban domin gabatar da ayyuka da
yawa. Wasu daga cikin kwamitocin kungiyar sun hada da


01 Kwamitin Da’awah.
02 Kwamitin Tarurrukan Wa’azi.
03 Kwamitin Kula da Marayu
07 Kwamitin Ilimi.
04 Kwamitin Mutane Goma.
05 Kwamitin Taimakon Gaggawa.
06 KWAMITIN ZARTASWA


Shugabanta na kasa a wannan lokaci shi ne Sheikh Abdullahi Bala Lau, khalifa na
farko a sashin shugabancin wannan kungiya tun bayan kafa kungiyar, wanda
tsohon mataimakin shugaban kungiyar ne a zamanin shugabancin marigayi Alh.
Musa maigandu Muhammad, kuma ya gaje shugabancin kungiyar ne bayan
rasuwarsa.


Alh. Ibrahim Na Alh. Azare: Mataimakin Shugaban Kungiya Na Kasa.
Sheikh Muhammad Kabir Haruna Gombe: Babban Magatakardan kungiya
Sheik Sani Yaya Jingir: Shugaban Majalisar Malamai na kasa
Sheik Yusuf Sambo Rigachuku: Mataimakin Majalisar Malamai na Kasa
Alh. Isa Waziri: Shugaban Yan Agaji na Kasa


Engr Mustapha Imam Sifti: Mataimakin Shugaban Rundunar Yan Aagaji na kasa
kungiyar ta samu karbuwa a sassa daban-daban na duniya. A Najeriya tana da
rassa a dukkanin jihohin Najeriya 36 da birnin tarayya. Haka kuma saboda irin
yadda kungiyar take kokarin ilmantar da al’umma, wannan ya sa har ta sami
kutsawa zuwa ga wasu kasashe, kamar su; Nijar da Mali da Sinigal da Togo da
Kamaru da Cadi da Burkina da Gini, Saudi Arabia da sauransu.


Wasu daga cikin abubuwan da kungiyar ta mayar da hankali wajen yin su, sun
hada da
Koyarwa a bisa tafarkin Manzon Allah (SAW) ba tare da bin son zuciya ko kuma
yin makauniyar biyayya ga wani ba.


Tsantsar karantar da hakikanin ilimin addinin Musulunci.
Gabatar da wa’azin kasa a duk makwanni biyu ko uku ko hudu don tunatar da
mutane abin da suka manta ko kuma lokutan da suka dace.


Kafa makarantu domin koyar da ilimin addini da na boko, da sauran fannonin
ilimi.


- Kai ziyarori gidajen marayu da gidajen yari da asibitoci, domin tallafar musulmai
marasa galihu.


Samar da taimakon gaggawa a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.
kungiyar ta samar da hamshaqan malamai a sassa wadanda suka sami daukaka ta
ilimi a fadin duniya baki daya, saboda jajircewa da kokarin bin tafarkin Manzon
tsira, Annabi Muhammad (SAW), sau da kafa.


Haka kuma ta ko wacce fuska tarihin izala zaizo , dogo ko gajere, ba za a taba
mantawa da irin gudummar da marigayi Sheikh Isma'ila Idris Bin Zakariyya ya
bada ba, da irinsu Marigayi Ibrahim Bawa Maishinkafa da Mal. Hudu Chikaji. Koda
ba manufarmu zayyana sunan kowa ba, amma muna addu'a ga dukkan wadanda
suka sadaukar da dukiyoyin su da kuma rayukansu akan wannan harka taci gaban
addini, Allah ya saka musu da gidan Aljanna ya hada mu dasu a babban matsayi a
lahira.


Wannan kadan ne daga cikin irin manufofin da kungiyar Izala ta kafu a kayi, kuma
a haka za'a tafi da ikon Allah.


Daga Karshe Muna Addu'an Allah ya nuna mana gaskiya gaskiya ce ya bamu ikon
binta, ya nuna mana karya karya ce ya bamu ikon guje mata Amin.


[audio mp3="https://www.mimbarinsunnah.com/wp-content/uploads/2020/04/Tarbiyyar-Yara-Amusulinci-Malama.mp3"][/audio]



 

 

 

 
Disqus Comments